For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaben 2023: Yanda Zan Magance Matsalar Tsaro Da Lagartaccen Tattalin Arzikin Najeriya – Atiku

Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar ya ce, gwamnatinsa zata magance matsalolin tsaron Najeriya ta hanyar daukar matakai masu tsauri idan har aka zabe shi a babban zabe mai zuwa.

Ana da kusan sauran watanni shida kafin babban zabe, dan takarar na PDP ya yi alkawarin bayar da fifiko wajen farfado da ‘lagartaccen’ tattalin arziki musamman ta hanyar shigo da kamfanoni masu zaman kansu.

Dan takarar dai ya yi wannan bayani ne a yau Talata a wajen taron Zauren Kamfanoni masu Zaman Kansu wanda Cibiyar Kasuwanci da Masana’antu ta Legos, LCCI ta gabatar a Lagos.

“Zamu dau matakai tsaurara kuma masu wahala a kan al’amuran matsalar tsaro ba tare da tsoro ko alfarma ba,” in ji Atiku wanda tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ne a tsakanin shekarar 1999 da 2007.

“Sanya hannun jari wata birkitacciyar dabba ce, kuma tana matukar tsoron tashin hankali da matsalar tsaro. Zan karya kalubalen ta hanyar sanya kudi a samar da ababan more rayuwa.”

Ya koka da yanayin talauci da tsananin rashin aikin yi, abun da ya ce suna cikin abubuwa da suke kara ruruta matsalar tsaro a kasa.

“Tattalin arzikin Najeriya rarrafe yake maimakon a ce yana girma. Samun kudin ‘yan kasa shine ma’aunin jin dadin ‘yan kasa, ya lalace a Najeriya tun shekarar 2015 saboda raguwar fitarwa da kuma karuwar yawan jama’a. Matsalar ‘yan Najeriya ta girmama a yanzu sama da yanda suke a 2015,” in ji shi.

Bangaren harkokin man fetur da gas, wanda shi ne kashin bayan tattalin arziki a Najeriya, ya samu gazawa a bangarori 19 cikin 30 daga shekarar 2014 zuwa yanzu.

Wannan ya kawo tsananin matsalar tattalin arziki ga bangarori da kuma ‘yan kasa da dama a tawon wannan lokaci.

“A wannan gwamantin mai ci, mutanenmu ba su da aikin yi. Sama da mutane miliyan 23 sun rasa aikinsu. A iya shekaru biyar, tsakanin 2015 da 2020, adadin wadanda suke aiki ya ragu da kaso 54%, daga miliyan 68 zuwa miliyan 31.”

Atiku Abubakar ya bayyana yawan wadanda ba su da aikin yi a Najeriya da cewa sun fi yawan mutanen Lagos ko mutanen da suke zaune a Birnin Tarayya, da kuma jihohin Abia, Bayelsa, Cross River, Ebonyi, Kwara da Nasarawa gaba daya.

Ya kara da cewa, mafi yawan wadanda ba su da aikin yin masu kananan shekaru ne maza da mata wadanda suka rasa samun hanyar rayuwa mai dadi da kuma kyakkyawan fata.

A karo na farko a tarihin Najeriya, kamar yanda Atiku ya fada, Najeriya na kashe kudi wajen biyan bashi sama da abun da take samu.

Ya ce, tuntuni Najeriya ta karya daya daga cikin ka’idojin cin bashi ta hanyar kashe sama da kaso 100% na kudin shigarta wajen biyan bashi.

Comments
Loading...