For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaben 2023: Yanzu Ba Juyinka Ba Ne, Peter Obi Ga Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi ya ce, zaben shugaban kasa da za a gudanar a shekarar 2023, ba za a yi shi ta hanyar duban kabila ko addinin ‘yan takara ba, saboda haka ba juyin wani ne daga cikin ‘yan takara ba.

Da yake jawabi a wani taron jam’iyyarsu kan shugabanci a yau Litinin wanda aka gudanar a Abuja, Obi ya yi alkawarin sanya hannu a alkawura tsakaninsa da Kungiyar Kwadago domin ganin duk abubuwan da aka tattauna a taron an bi su yanda ya kamata.

Da yake magana a kan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Obi ya nanata cewa tunda dai babu wani waje da Musulmi ko Kiristoci ke siyan abu da araha, ko Yarabawa ko Hausawa suna da wuta kyauta sama da saura a kasa, to zabe mai zuwa za a gina shi ne kan halayya da kuma cancanta ba wai don juyin wasu ne ba.

Obi na yin wannan shagube ne saboda jiyo dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu na ikirarin cewa, wannan karon juyin mulkin Najeriya na Yarabawa ne.

Dan takarar shugaban kasar ya kuma bayyana cin hanci da rashawa a matsayin ruwan dare a Najeriya saboda da shugabanni a cikin masu yi, “Idan shugaba ba ya sata, sannan ‘yan uwansa da suka zagaye shi ba sa sata da mun rage cin hanci da kaso 70%. Na yi gwamna na tsawon shekaru takwas, babu inda aka samu wani kudi ya bata.

Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Jam’iyyar LP na Kasa ya ce, yanzu lokacin da ya dace a Najeriya a kara duban yanda ya kamata siyasa ta kasance, inda ya jaddada cewa matsalolin da ake fuskanta yanzu sun samo asali ne daga rashin iya shugabanci.

Comments
Loading...