Mu matasa mune abun babban alfaharin kowacce al’umma a fadin duniya. Matasa mune ke kan gaba wajen yin aiki tukuru domin samawa al’ummar mu kyakkyawar makoma da zata kawo cigaba mai dorewa.
Wannan ne yasa ake mana lakabi da shugabannin gobe domin ana sa rai mune zamu maye guraben iyayen mu, kakanni, malaman mu da shugabannin mu, idan sun shude mu cigaba da tafiyar da harkokin su akan tsare tsare da kuma kyawawan manufofi.
Rike ragamar jagorancin al’umma tana samuwa ne idan mu matasa mun sami horo da kwarewa sosai a fannonin ilmi da rayuwa daban daban masu muhimmaci. Sai dai idan mukayi duba na tsanaki zamu ga matasan mu musamman na arewacin Najeriya anyi mana nisa fintinkau wajen sanya kishin al’ummar mu a dukkan bangarori da fannonin rayuwa, musamman a siyasan ce.
KU KARANTA: Wanda Ya Kamata Ya Zama Gwamnan Jigawa A 2023 – Ahmed Ilallah
Yankin Arewacin Nigeria yana fama da matsaloli iri-iri da suka zamewa yankin alakakai da yi masa tarnakin da kawo cikas ga cigaban yankin da al’ummar yankin baki daya. Wadannan sun hada da rashin ayyukan yi da ya ke haifar da zaman kashe wando ga dimbin matasan, talauci dake haifar da neman kudi ta koyaya, ya ki halak ya ki haram, koma bayan harkokin ilimi, matsalolin tsaro, matsalolin tattalin arziki, kiwon lafia da rashin samun shugabanni da jagorori na kwarai, da dai sauran abubuwan kyautata rayuwar al’umma.
Babban abunda ya kamata mu matasa mu saka a gaba shine; matakan da ya kamata a dauka domin magance wadannan matsaloli da suke ci mana tuwo a kwarya. Sai dai maimakon haka mu matasa musamman na Arewa yanzu munfi mayar da hankalin mu wajen kare muradun iyayen gidan mu a siyasance fiye da muradun jama’a ta yadda ake amfani da mafiya yawan mu wajen cimma burin siyasa ko wasu boyayyun manufofi wanda wannan ba abune mai kyau ba.
A bisa wannan dalilai ya zama dole mu matasa mu zage dantse da tashi tsaye haikan na ganin mun matsa lamba ga gwamnati da masu fada aji kama daga sarakuna, yan kasuwa, yan boko, yan siyasa da malaman addini da su tashi tsaye haikan suyi kira da babbar murya domin kwato matasa daga wannan halin da muke ciki domin samar da kyakyawar goben al’umma mai dorewa a wannan zaben da muke tunkara a 2023.
Matasa na bayar da gudunmawa sosai wajen zakulo shugabanni wanda suke da kwarewa da tausayin al’umma tare da basu gudunmawar kaiwa ga samun nasara domin kyakyawar goben al’ummar baki daya. Allah ya bamu shugabanni na kwarai masu kaunar mu, da cigaban kasar mu baki daya ameen.
Ibrahim Rabiu Birnin Kudu
rabiu022@gmail.com