For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zabtarewar Kasa A Malesiya Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 8

Kimanin mutane takwas ne rahotanni ke cewa sun mutu da sanyin wannan safiya wannan Jumma’a a tsibirin Genting na kasar Malesiya, sakamakon iftila’in zaftarewar kasa.

Bayanai na cewa akwai ma wasu sama da mutum 50 da suka bace bayan faruwar lamarin a wani yanki da ke samun bakuncin masu yawon shakatawa.

Kimainin mutane 80 ke a wajen lokacin da ibtila’in ya faru, kuma jami’ai na cewa an yi nasarar ceto mutane 23 kawo yanzu.

Tsibirin Genting dai na cikin gundumar Selnagor da ke da karfin arziki a Malesiya, kuma a baya ya sha fama da bala’in zaftarewar kasar.

Tsibirin da ke da kyawun gaske ga mutane daga sassa daban-daban na duniya na zuwa ziyarar kashe kwarkwatar ido.

Comments
Loading...