Dadaddiyar matsalar zagwanyewar ma’aikata a bangaren kula da lafiyar ‘yan Najeriya ta kara kamari a kasar, inda a yanzu likita daya ke daidai da marassa lafiya 10,000, lamarin da ya saba da bukatar Hukumar Lafiya ta Duniya na likita daya ga majinyata 1,000.
Wadannan alkaluma dai sun fito ne daga National Institute for Policy and Strategic Studies (NIPSS) da ke kula da yanayin tsare-tsare da kuma gudanar da al’amura a Najeriya.
Kididdigar ta kuma nuna cewa, a yanzu haka Najeriya ce kasa ta uku da ke da yawan likitoci masu aiki a kasar Birtaniya baya da kasar India da Pakistan.
Babban Daraktan NIPPS, Farfesa Ayo Omotayo ne ya bayyana hakan a jiya, a wajen wani taron wayar da kai kan zagwanyewar ma’aikatan lafiya da kuma tasirinsa a wajen samar da ingantacciyar kulawar lafiya ga kananan yara da kuma iyali.
Ayo ya ce, “Najeriya ta rasa likitoci sama da 9,000 wadanda suka yi kaura zuwa Birtaniya, Canada da Amurka a tsakanin shekarar 2016 da 2018, inda ya kara da cewa, likitoci 727 ne wadanda suka sami horo a Najeriya suka yi kaura zuwa zuwa Birtaniya cikin watanni 6, tsakanin watan Disamba na 2021 zuwa watan Mayu na 2022.”
Ya kuma ce, “Bayanai daga rijistar Hukumar Kula da Ma’aikatan Jinya da Unguzoma ta Birtaniya sun nuna cewa, adadin ma’aikatan jinya da ungozoma da suka sami horo a Najeriya ya karu da kaso 68.4 daga ma’aikata 2,790 a watan Maris na 2017 zuwa 7,256 a watan Maris na 2022.”