Jagoran Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Tinubu a yau Litinin ya ce ya sanar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari burinsa na yin takarar shugaban kasa a zaben 2023 mai zuwa.
Tinubu ya ce, wannan dadadden burinsa ne na rayuwa, sannan kuma yana da kwarin guiwa, basira da karfin iya dorawa kan hangen Shugaba Buhari.
Jagoran jam’iyyar ta APC ya bayyana hakan ne yau a Fadar Shugaban Kasa bayan ganawa da yai da shugaban a boye a Abuja.
KU KARANTA: Buhari Ya Ki Bayyana Wanda Yake So Ya Gaje Shi Saboda Kariya
Ya ce, ya je Fadar Shugaban Kasar ne domin ya gana da Shugaban Kasa kan al’amuran da suka shafi Najeriya da suka hada da abubuwan da suke faruwa a jam’iyyar APC da ma matsalolin tsaro.
Da yake amsa tambayar da akai masa, ko ya fadawa Shugaba Buhari kudirinsa na neman shugaban kasa a shekarar 2023, ya bayyana cewa, “na fadawa Shugaban Kasa kudiri na, amma har yanzu ban fadawa ‘yan Najeriya ba, ina cigaba da tuntuba.”
Da aka tambaye shi ko me Shugaba Buhari ya ce masa kan batun, Tinubu ya ce, shugaban kasa dan demokaradiyya ne kuma bai ce ya dakata kan kudirinsa ba.