For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zamu Bar Nigeria Sama Da Yanda Muka Sameta – Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa ‘yan Nigeria cewa gwamnatinsa ta shirya tsaf wajen tabbatar da cewa ta bar Nigeria sama da yanda ta sameta, inda yai kira ga ‘yan Nigeria da su yi adalci kan nasarorin da gwamnatinsa ta cimma.

Shugaba Buhari ya bukaci ‘yan Nigeria da su tantance kokarin gwamnatinsa gwargwadon alkawuran yakin neman zaben da yai kafin zaben 2015.

Ya yi wannan jawabin ne a lokacin ziyarar da ya kai Kaduna ta kwanaki biyu domin kaddamar da aiyuka a Kafanchan, Kaduna da kuma Zaria.

Da yake jawabi a Fadar Sarkin Jema’a, Alhaji Muhammadu Isa ll, a Kafanchan, Shugaba Buhari ya bayyana kudirinsa na inganta tsarin siyasar Nigeria domin samun cigaban rayuwar al’umma.

Shugaban ya kuma yi jawabi kan amfani da ‘yansanda da sojoji wajen magance matsalar tsaro, sai dai kuma ya bukaci ‘yan Nigeria da su amincewa jagorori wajen samar da yanayi mai kyau.

“Babu wanda za a bari ya samar da rundunar batagari domin ya takurawa al’umma. Ya kamata kowa ya san da haka,” in ji Shugaba Buhari.

Comments
Loading...