Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya ce gwamnatinsa zata kori karin wasu malaman makarantun sikandiren jihar wadanda ba su cancanta ba a shekarar nan.
El-Rufa’i ya baiyana hakan ne lokacin da yake nuna korafinsa kan cewa, wadansu malaman sikandiren shaidar kammala firamare kawai suka mallaka amma kuma suna koyarwa a makarantun gwamnati.
Ya baiyana hakan ne a yau Alhamis a yayin jin ta bakin ma’aikatu da maaikatan yada labarai na fadar Shugaban Kasa ke shirya mako-mako a Abuja.
El-Rufa’i ya baiyana cewa gwamnatinsa ta debi mutane da yawa aiki sama da adadin wadanda ta kora cikin shekaru 5.
“Mun debi sama da sabbin ma’aikata 40,000 cikin shekaru 5 da suka wuce, mafi yawancinsu ma’aikatan jinya, ungozoma da kuma malaman makaranta,” in ji El-Rufa’i.
Ya baiyana cewa, a daidai lokacin da yake jawabi, gwamnatinsa ta debi kwararrun malaman sikandire guda 7,700 wadanda za a tura ajuzuwa da zarar an gama zakulo wadanda ba su cancanta ba daga cikin wadanda ke kotarwa a makarantun a halin yanzu.
El-Rufa’i ya kara da cewa, babban burinsa shine bunkasa makarantun gwamnati a Kaduna, ta yanda za su yi ingancin da zai iya sanya dansa a ciki.
Ya kuma baiyana cewa duk da cewar a baya ya sanya dansa a makarantar gwamnati, ya mayar da shi gida saboda barazanar za ai garkuwa da shi, abinda kan iya jefa sauran dalibai cikin hatsari.
(PUNCH)