For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zamu Magance Matsalar Tsaro, Mu Gyara Tattalin Arziki – Kwankwaso

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce, gwamnatinsa zata magance matsalar tsaro sannan ta farfaɗo da tattalin arziki idan har aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a shekarar 2023.

Kwankwaso ya baiyana hakan ne jiya Litinin a Calabar lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar, bayan ya samu nasarar zama ɗan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar.

“Zamu magance matsalar tsaro kamar su matsalar ƴan bindiga, da sauransu,” ya kuma ƙara da cewa, zai “dawo da kimar tattalin arzikin ƙasa” kuma sannan jam’iyyar “NNPP zata tabbatar da haɗin kan ƙasar nan”.

Ya kuma ce, jam’iyyar na da nagartattun mutane kuma waɗanda zasu iya jagorantar ƙasa, sannan ya buƙaci magoya bayan da su je su yanki katin zaɓe a matsayin shiryawa babban zaɓe mai zuwa a baɗi.

Ya ce, jam’iyyar ta yi nasarar mamaye ƙasa da samar da shugabanci a dukkanin ƙananan hukumomi da ƙasar nan.

Tun a farko dai, shugaban jam’iyyar na Jihar Anambara, Tony Odey, ya baiyana Kwankwaso a matsayin mai samar da nutsuwa da ya zo domin ya samar da jin daɗi ga ƴan Najeriya.

Ya ce, Kwankwaso zai yi wa Najeriya manyan aiyukan da yai a Kano lokacin yana gwamna, matuƙar aka zaɓe shi.

Comments
Loading...