Daga: DailyTrust
Sabon zababben shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Iyorchia Ayu, ya bayyana cewa zai samar da sasanto domin samar da hadin kan jam’iyyar don kayar da jam’iyya mai Mulki All Progressives Congress (APC) a shekarar 2023.
Ayu, ya yi wannan maganar ne lokacin zaman nuna murna da wakilan jam’iyyar PDP daga jiharsa ta Benue a ranar Lahadi a Abuja, ya ce zai yi aiki tukuru domin hada kan jam’iyyar domin samun damar karbar shugabancin kasa a 2023.
Sai dai jam’iyyar APC ta ce wannan abu ne ba mai yiwuwa ba jam’iyyar PDP ta kayar da APC a 2023.
Ayu ya ce, tunda sasanto ne ya samar da shi ba tare da hatsaniya, saboda haka hanya ce da ta dace ai amfani da ita har ma a gurbin takarar shugaban kasa idan jam’iyyar PDP ta amince.
“Akwai aiki da yawa da za mu yi. Kamar yanda muka yi a 1998, za mu maimaita hakan,” in ji shi.
Sabon shugaban jam’iyyar ya fadawa masu sukarsa cewa kar su yi tunanin zai yi watsi da tsarinsa na rayuwa wanda ya ce na tsayawa kan gaskiya ne koyaushe kuma kowa za ta shafa.
Ya kuma shawarci wadanda suka shiga siyasa domin samun abin duniya da su koma kasuwanci maimakon siyasa, saboda siyasa ana yin ta ne domin bautawa kasa.
Ya yabi kowanne daga cikin masu ruwa da tsaki wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen zamansa shugaban jam’iyyar PDP, inda ya kara da cewa, shugabancinsa zai mayar da hankali kan mata da matasa saboda sune ke rike da makullin samun nasarar zabubbuka.
Ayu ya kuma musa cewa Sanata David Mark ya nemi takarar shugabancin jam’iyyar, inda ya ce Sanata Mark ya goyi bayansa tun daga farkon lamari wanda hakan ya ba shi nasarar zama shugaban jam’iyyar PDP na kasa.
Haka kuma, Gwamna Samuel Ortom ya fada a taron tattaunawar cewa, tsarin samar da sasanto za a bi domin fitar da dantakarar gwamna a 2023 a jihar Benue bayan an tuntubi duk masu ruwa da tsaki.
Lokacin da akai tuntuba domin jin ba’asi, Mataimakin Kakakin Jam’iyyar APC na kasa, Yekini Nabena ya ce, “Abu ne da ba zai yiwu ba. Batu ne na yawa. Daga ina za su samu yawan?
“Da yawa daga gwamnoninsu za su dawo APC, saboda haka ra’ayin kansa ne kawai; amma ya kamata su tuna cewa APC ba bacci take ba.”