Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a shirye yake ya sanya hannu a gyaran dokar zabe idan har Majalissar Dokoki ta Tarayya ta yi wasu gyare-gyare.
Shugaban ya bayyana cewa, canje-canjen da za ai su kunshi bayar da dama ga jam’iyyun siyasa su zaba tsakanin ‘yar tinke, amfani da delegets ko kuma sasanto a yayin fidda ‘yan takarkaru.
Shugaban ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da gidan Talabishin na Channels wadda Maupe Ogun da Seun Okinbaloye suka yi da shi aka yada a ranar Laraba.
“Abin da na ce (shi ne) ya kamata a samu damar zabi,” in ji Buhari.
“Bai kamata mu takura kan cewar dole sai an yi ‘yar tinke ba, ya kamata a samu amfani da delegets da kuma sasanto.”
Da aka tambaye shi, ko zai sanya hannu idan ‘yan majalissar suka yi gyare-gyaren da yake magana, shugaban ya ce, “e, zan sanya hannu.
“Ya kamata a samu damar zabi, ba ka takurawa mutane ba kuma ka ce demokaradiyya kake yi. Ka ba su damar zabi saboda su bi zabinsu.”