For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Bai Wa Fannin Tattalin Arziki Muhimmanci – Dan Takarar Gwamnan Jigawa Na APC

Dan takarar gwamnan Jihar Jigawa na jam’iyyar APC, Umar Namadi, ya ce babban burinsa idan ya ci zaben shi ne ya bunkasa tattalin arzikin jihar.

Ya bayyana haka ne a hira ta musamman da BBC Hausa.

“Abin da ya ba ni kwarin gwiwa na shiga wannan takara shi ne yadda a shekara bakwai da suka wuce mun yi aiki da shugabana Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, na ga irin dimbin ci gaban da aka kawo wa jihar Jigawa a wannan lokaci, sannan kuma na san irin tunaninsa da kuma abin da yake so jihar Jigawa ta zama.

Saboda haka wannan ya ba ni kwarin gwiwar cewa ya kamata ni ma na bayar da tawa gudunmawar na dora kan abubuwan da wannan mutumin ya yi.”

Umar Namadi ya kara da cewa “Na farko dai muna so mu ga cewa an dora tattalin arzikin Jihar Jigawa a kan wani tafarki mai dorewa,” inda yai alkawarin cewa, a shekaru biyu na farkon mulkinsa idan ya ci zabe, zai mayar da jihar mai iya samarwa kanta akall kaso 50% na abun da gwamnatin tarayya ke ba ta.

A fannin barakar da ke jam’iyyarsu ta APC a Jigawa, biyo bayan zaban fidda gwanin da ya ba shi nasara, Namadi ya ce, babu baraka a jam’iyyar, domin har yanzu cikin ‘yan takara 8 da suka nemi takarar gwamna tare da shi, babu wanda ya fice daga APC.

Comments
Loading...