For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Baiwa Masu Tsohon Kudi Damar Canja Kudinsu Idan Na Ci Zabe – Kwankwaso

Ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce baya goyon-bayan tsarin da aka bi wajen sauya takardun kuɗi a Najeriya.

Kwankwaso da ke shaida hakan a lokacin wata tattaunawa da BBC, ya ce yanzu abu guda shi ne mahukunta a kasar su kokarta su kara wa’adin da babban bankin kasar ya bayar na daina amfani da tsoffin takardun kuɗi.

Injiniya Kwankwanso ya ce al’umma na shan wahala sakamakon canjin kuɗin, don haka ya kamata gwamnati ta sassauta

Kalaman ɗan takaran na zuwa ne kwanaki kadan wa’adin da babban bankin Najeriya wato CBN ya bayar na daina karban tsoffin kuɗi ya cika.

Sai dai dɗn takarar ya ce idan gwamnatin APC mai Mulki ta ƙi kara wa’adin, kada kowa ya ta da hankalinsa.

Injiniya Kwankwaso ya ce masu kuɗi su ajiye kudinsu, idan ya samu nasarar zama shugaban  kasa zai bai wa kowa damar canja kuɗinsa ba tare da kwabonsa ya yi ciwon kai ba.

Ina Takaicin Ganin Ana Wahalar Da Talaka

Dan takarar ya ce abu ne na takaici a fito da wannan tsari a yanzu cikin kuraran lokaci ba tare da bai wa mutane wa’adin mai tsayi na sauyin kudadensu hankali kwance ba.

Kwankwaso ya ce su dai nasu bai wuce bai wa gwamnati hakuri ba, na ta dubi talakan Najeriya ta jikansu kada mutane su yi asara.

“Talaka musamman na arewa na cikin masifa da matsi na rayuwa da kullum ake ganin sabon salo.

Sai dai kuma Kwanwkaso ya ce idan gwamnati tayi biris, to zai yi fatan nasarar zaɓe domin ya maidowa mutane halaliyarsu ba tare da ko sisinsu ya salwanta ba.

Dan takarar ya ce a tsari mai inganci ana bai wa mutane wa’adi mai tsayi idan aka sauya kudi, ba wai komai a yi shi cikin kuraren lokaci ba, kuma babu sassauci.

Injiniya Kwankwaso ya ce duk wadannan sauye-sauye da matakai kan talakan Najeriya ya ke karewa, don haka lokaci ya yi da talaka zai yiwa kansa gata.

“Babu dalilin da gwamnati za tayi biris da shawarwarinsu da kuma na al’umma.

“Ba laifi ba ne samar da hanyar da kowa zai kai kuɗinsa banki a biya shi ba tare da ya yi asarar ba”.

“Shiyasa inda Mulki ya dawo hannumu za mu fitar da tsarin da zai bai wa kowa damar zuwa banki ya mayar da kuɗinsa a ba su hakkinsu, in ji Kwankwaso.

Injiniya Kwankwaso ya ce da shi ke mulkin kasar na da ba zai goyi bayan canji kuɗi ba a wannan lokaci.

Amma yanzu shawarasa shi ne mutane su ajiye kuɗinsu da katunan zaɓensu, idan suka jefa musu kuri’a dukiyarsu zata dawo.

A ranar 31 ga watan Janairun 2023, wa’adin daina karbar tsoffin takardun kuɗin naira ke cika, kuma ga dukkan alamu bankin Najeriya ba shi da niyyar tsawaita kwanaki.

Kungoyoyi da daidaikun mutane da ‘yan siyasa na ta shawarata karin wa’adi saboda koken da al’umma musamman ‘yan kasuwa ke yi.

Sai dai da alama babu wani sauyi ko tsawaita wa’adi da gwamnati ke da niyya.

BBC Hausa

Comments
Loading...