For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Biyawa Kowanne Yaro WAEC In Na Zama Shugaban Kasa – Tinubu

Daga: Haruna Ahmad Bultuwa

Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, ya yi alkawarin biyawa duk wani yaron Najeriya kudin jarrabawar kammala sakandire ta Afirka ta Yamma, WAEC, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da jaridar The Nation ta kalla a ranar Larabar nan.

Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar APC.

A jawabin nasa, jigo a jam’iyyar APC ya ce, “za mu biya kudin jarrabawar ‘ya’yanku ta Afirka ta Yamma, ta yadda ba za a bar kowa a baya ba, komai talauci.

“Muna bukatar kwanciyar hankali a kasar. Muna buƙatar zaman lafiya kuma dakatar da ƴan fashi. Yana da matuƙar mahimmanci domin mata sune waɗanda ke fama da matsalar fashi, tashin hankali, da rashin zaman lafiya. Idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali, ba za mu iya gina kasa cikin sauri ba” inji Bola Tinibu.

Comments
Loading...