Dan takarar jam’iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA) a zaben gwamnan jihar Anambra mai zuwa, Farfesa Chukwuma Soludo, ya bayyana cewa burin sa shine ya zama wanda ya lashe zabe da kuri’u miliyan daya.
Ya bayyana cewa duba da manyan nasarorin da gwamna mai barin gado, Willie Obiano ya samu tare da kwarewarsa da gogewarsa a cikin aikin gwamnati, tabbas zai sami kuri’u da yawa a zaben.
Soludo ya kuma ce; “Muna da tsarin samar da ayyukan yi har 130,000 a kowace shekara”.
Ya yi watsi da jita-jitar da ke cewa domin jihar ta kasance mai samun goyon bayan gwamnatin tarayya, akwai bukatar samun gwamna daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulkin tarayya, yana mai bayyana cewa a halin yanzu yana cikin masu rike da mukamai a gwamnatin tarayyar.
Ya kara da cewa mafi yawan wadanda ke fafatawa da shi ba su da kakkarfar damar da yake da ita a fadar shugaban kasa.
Matar marigayi mataimakin shugaban kasa a jamhuriya ta biyu, Alex Ekwueme, Misis Ifeoma Ekwueme, ta bayyana cewa burin mijinta ne tsohon shugaban Babban Bankin Najeriyar, Farfesa Chukwuma Soludo ya mulki jihar Anambra.
Gwamna Obiano ya bukaci al’ummar jihar da su zabi Soludo a matsayin wanda zai gaje shi, inda ya ce Soludon zai yi abin da ya fi na shi.