For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Haɗa Kan Ƴan Najeriya, Na Magance Matsalar Tsaro, Na Kuma Ciyar Da Tattalin Arziki Gaba – Atiku Abubakar

A lokacin jawabin karɓar nasarar da yai a zaɓen fidda gwanin da zai yi wa jam’iyyar PDP takarar Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar wanda ya lashe zaɓen ya baiyana cewa zai haɗa kan ƴan Najeriya tare da kawo ƙarshen rarrabuwar kan da ake ciki.

Atiku ya kuma ce, yana bukatar goyon bayan sauran ƴan takarar da ba su yi nasara ba, sannan zai yi aiki tare da su wajen ganin jam’iyyar PDP ta samu nasara a 2023.

Ya kuma baiyana zaɓen fidda gwanin a matsayin sahihi kuma mafi inganci wanda jam’iyyar PDP ta taɓa yi.

Atiku Abubakar ya ce, idan har aka zaɓeshi Shugaban Ƙasa to zai haɗa kan ƴan Najeriya sannan ya yi maganin matsalar tsaro ya kuma bunƙasa tattalin arzikin Najeriya.

Ya kuma ƙalubalanci jam’iyyar APC da wargaza kan ƴan Najeriya, inda ya ce ya yi alƙawarin haɗa kan ƴan Najeriya.

Atiku ya kuma ce, samun haɗin kai a wannan lokacin yana da matuƙar muhimmanci, saboda jam’iyyar APC ta wargaza kan ƴan Najeriya gaba ɗaya.

Comments
Loading...