For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2027, PDP Ta Riga Ta Mutu – Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya nuna tabbacin lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 ƙarƙashin jam’iyyar, ya bayyana ne hakan a ranar Asabar yayin ƙaddamar da sakatariyar NNPP da ke kan titin IBB a Katsina.

Tsohon Gwamnan Kano ya ziyarci Katsina ne domin yi wa iyalan Yar’Adua ta’aziyya kan rasuwar mahaifiyarsu, Hajiya Dada.

Ya ce jam’iyyar NNPP ta shirya tsaf don karɓar mulkin ƙasa, jihohi da sauran muƙamai a faɗin Najeriya a shekarar 2027.

Kwankwaso ya ƙara da cewa jam’iyyar PDP ta mutu, saboda ficewar da suka yi daga jam’iyyar bisa rashin tsari.

Shugaban NNPP na Katsina, Alhaji Armaya’u Abdulkadir, ya jaddada buƙatar faɗakar da jama’a kan sabon tambarin jam’iyyar wanda ke nufin samar da ilimi ga kowa da kowa.

Comments
Loading...