Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabbatar da cewa, samar da ƴansandan jihohi wani muhimmin abu ne wajen magance matsalar tsaro a Najeriya.
Tambuwal ya baiyana hakan ne a hirarsa da gidan talabijin na CHANNELS ta cikin shirin Politics Today na jiya Talata.
Ya jaddada cewa, idan har ya zama Shugaban Ƙasa a shekarar 2023, zai tabbatar da an samar da ƴansandan jihohi a dukkanin faɗin Najeriya.
“Ina da masaniyar yanda ya kamata a yi (domin magance matsalar tsaro),” in ji shi.
“Dole ne mu kusantar da batun kusa da al’umma. Dole ne mu je mu yi maganar ƴansandan jihohi, mu kai tsaro kusa da al’umma.”
Da yake amsa tambayar ko zai gabatar da ƙudiri ga Majalissar Tarayya kan buƙatar samar da ƴansandan jihohin a matsayinsa na Shugaban Ƙasa, Tambuwal ya ce, “Ko da kuwa hakan na nufin, ni Aminu Tambuwal a matsayin Shugaban Ƙasa zan ɗau ƙudirin da kaina zuwa Shugaban Majalissar Dattawa da Kakakin Majalissar Wakilai, zan yi hakan,” in ji shi.
“Saboda na yi imanin cewa, yana ɗaya daga cikin gudunmawar da muke buƙata ta gaggawa wajen murƙushe matsalar tsaro a ƙasar.”
Tun farkon hirar tasa da CHANNELS, Tambuwal ya ƙalubalanci batun karɓa-karɓa, inda ya ce, cancanta ake buƙata ba ɓangaranci ake buƙata ba wajen zaɓin Shugaban Ƙasa.
Ya kuma baiyana cewa yana tuntuɓar sauran ƴan takarar Shugaban Ƙasa a jam’iyyar PDP domin samun sasanto.