For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zan Tattauna Da ‘Yan IPOB Idan Na Ci Zabe – Peter Obi

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce idan ya ci zaben shugaban kasa a 2023, zai tattauna da ‘yan haramtacciyar kungiyar nan ta masu fafutukar neman ‘yancin Biafra (IPOB) da sauran masu fafutuka domin maido da zaman lafiya kasar.

Obi ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da jaridar Daily Trust a Abuja yayin da yake amsa tambaya a kan matsalar tsaro a Najeriya.

Dan takarar wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne, ya ce salonsa zai zama daban da na takwarorinsa kan wannan matsala idan har aka zabe shi a ranar 25 ga watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

Obi ya ce, ya sha nanatawa ba sau daya ba ba sau biyu ba, cewa Najeriya ba ta da masu fafutuka fiye da kasar Brazil.

”Idan kana so zan nuna maka kasashen da suka yi fama da masu fafutuk a baya, ko Brazil ce ko Mexico ce, ko wacce ce.

”A kudu maso gabashinmu, abu ne mai sauki, zan yi tattaunawa, zan tattauna, demokaradiyya ce kuma a mulkin demokaradiyya kana mulki ne da cimma matsaya. Idan wani ya ce ba ya jin dadi, sai ka kira shi ka zauna da shi ka tattauna da shi,” in ji Obi.

Comments
Loading...