For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

‘Zanga-Zanga Ba Cin Amanar Kasa Ba Ne’, Baturen Birtaniya Ya Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Zargin Juyin Mulki Ga Tinubu

Baturen Birtaniya da ake zargi da tayar da fitina a kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, Drew Povey, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ka da ta dauki zanga-zanga a matsayin cin amanar kasa.

Mista Povey, wanda gwamnatin Najeriya ta ce yana da suna biyu, Drew Povey ko Andrew Wynne, ya fitar da wannan jawabi a matsayin martani ga zargin gwamnati na cewa yana “gina hanyar da zata kawo juyin mulki” ga gwamnatin Bola Tinubu “tare da jefa kasa cikin rudani.”

Gwamnati ta yi bincike da rufe shagonsa na littattafai da ke a hedkwatar Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da ke Abuja.

Daya daga cikin tuhumetuhumen da ake yi masa shi ne taimaka wa wasu masu zanga-zangar #EndBadGovernance da nufin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Cikin jawabin da aka fitar daga ofishinsa, ya ce: ZANGA-ZANGA BA CIN AMANAR KASA BA CE – a saki duk wadanda ake tsarewa! Zanga-zangar #EndBadGovernance da #EndHunger sun tsorata gwamnati, amma maimakon gwamnatin ta biya bukatun jama’a, sai ta koma yin zalunci.

“Akwai yiwuwar jami’an tsaro sun kashe mutane 40 a lokacin zanga-zangar, kuma an kama dubban mutane, daga cikinsu akwai wadanda har yanzu suna tsare. A Abuja, mahukunta sun kai hari kan wadanda ake kira shugabannin shirya zanga-zangar. Mutane goma suna fuskantar tuhume-tuhumen da ba su da tushe ciki har da cin amanar kasa, yin tawaye da kuma tayar da yaki da gwamnati.

“NLC ta yi alkawarin yin yajin aiki na gama gari don kare shugabanta, Joe Ajaero, daga kamu da tsarewa bisa irin wadannan tuhume-tuhumen. Duk da rashin kwararan hujjojin da ake da su kan wadanda aka kama, suna fuskantar shekaru masu tsayi a kurkuku sai dai idan kungiyar kwadago ta shirya tsayawa don kare su. A ranar 7 ga Agusta, NLC ta ce tana ‘Allah wadai da cin zarafin dan Adam da jami’an tsaro suka yi wa masu zanga-zangar lumanar.’

“Mutumin farko da aka kama a wannan lamari shi ne Eleojo Opaluwa. Tsohon abokin aiki ne na Joe Ajaero, yana aiki a NUEE, kungiyar ma’aikatan lantarki, a matsayin mai shirya zanga-zanga a Abuja. Kuma shi ne Mataimakin Shugaban NLC a Jihar Kogi. An tsare shi tsawon makonni hudu ba tare da wata hujja ba. An shaida wa iyalinsa cewa ya karbi sakon WhatsApp daga daya daga cikin sauran shugabannin da ake zargi. Wannan kuwa bayan an riga an kama Eleojon.

“Wadanda ake tsare da su guda goma suna fuskantar zargin hadin kai wajen aikata manyan laifuka. Amma ba su san juna sosai ba. Biyar daga cikinsu na iya kasancewa mambobin wata kungiyar WhatsApp da aka kafa don shirya zanga-zangar a Abuja. Amma biyar din da sauran ba su san wadannan abokan zanga-zangar ba. Wata kila su ne masu tutar zanga-zanga daga Kano da aka hada domin ƙara yawan wadanda ake zargin da shirya zanga-zangar a Sokoto zuwa Maiduguri.

“Akwai rashin jituwa tsakanin gwamnati da ‘yansanda da ke gudanar da wannan bincike. Shugaban sashin Intelligence Response Team (IRT) ya shaida wa lauyoyin wadanda ake tsare da su cewa zai sake su, amma ya samu umarni daga sama na kar ya sake su. Saboda haka, ‘yansanda sun yi wani abu da ya zama kamar na rashin gaskiya, wanda ya shafi mamallakin Iva Valley Books. Suna ikirarin cewa yana amfani da suna Andrew Povich, suna mai kama da na Rasha, kuma ya bar Najeriya zuwa kasar Rasha.

“Duk wadannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne. Yomi, wanda ke aiki da Iva Valley Books, ya fuskanci mummunan hali kamar sauran wadanda ake tsare da su. An kama shi a gaban matarsa da ‘yarsa ‘yar shekara uku. An kwace dukkan wayoyinsu, duk da rokon da matarsa ta yi na cewa suna bukatar waya don neman kudin abinci.

“An tsare shi ba bisa ka’ida ba tare da daure shi da sarƙa, an doke shi kuma an yi masa azaba na tsawon kwana uku. Abin da ya hada shi da wannan zanga-zanga kawai shi ne tsara takardun talla da aka buga domin zanga-zangar bisa umarnin maigidansa. NLC ta nuna cewa tana da karfin kare shugabanta, saboda haka, yanzu tana bukatar fadada wannan tsari don kare sauran jami’anta, membobinta, da kuma jama’a baki daya.”

Comments
Loading...