For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zanga-zangar Yunwa: Gwamnati Zata Gurfanar da Masu Zanga-Zanga, Ciki Har da Ɗan Birtaniya a Yau

Gwamnatin Tarayya zata gurfanar da wasu masu zanga-zanga, ciki har da wani ɗan ƙasar Birtaniya, Andrew Wynne, bisa rawar da suka taka a zanga-zangar yunwa da aka gudanar kwanan nan, inda take zarginsu da aikata cin amanar ƙasa da kuma yunƙurin tada zaune tsaye a ƙasa.

Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya gabatar da tuhume-tuhume guda shida a kan waɗanda ake zargin, yana iƙirarin cewa an yi zanga-zangar ne don razana shugaban ƙasa da kuma tada zaune tsaye ta hanyar kai hari kan jami’an ‘yan sanda da kuma lalata dukiyoyin gwamnati.

Zanga-zangar ta #EndBadGovernanceInNigeria, ta ɗauki tsawon kwanaki inda aka gudanar da ita daga 1 zuwa 10 ga watan Agusta, 2024, ta kuma faru ne sakamakon yanayin tattalin arziki da ke ƙara tabarbarewa.

A cewar lauya mai kare hakkin ɗan Adam, Femi Falana, sama da mutane 2,000 aka kama yayin zanga-zangar, kuma da dama daga cikinsu sun kasa samun wakilcin lauyoyi.

Ana zargin waɗanda ake tuhuma da haɗin gwiwa da wasu kasashen waje don yin yaƙi da ƙasa, kuma ana kallonsu hakan a matsayin barazana ga tsaron ƙasa.

Wannan shari’ar dai ta haifar da muhawara mai zafi a faɗin kasar nan kan batun samar da tsaro da kuma tabbatar da ‘yancin ‘yan kasa.

Comments
Loading...