For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zaɓen 2027: Ko Jam’iyyun Adawa Zasu Iya Haɗa Kai Su Ƙalubalanci APC?

A halin yanzu, kowanne daga cikin manyan jam’iyyun adawa irin su Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP), All Progressives Grand Alliance (APGA), New Nigeria Peoples Party (NNPP), da African Democratic Congress (ADC) suna fama da matsalolin cikin gida da ke barazana ga cigabansu.

Kwanan nan, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Mr Peter Obi, ya gana da abokin takararsa na NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a 2023.

Wannan ganawar ta kasance wani bangare na shirin haɗa kai na siyasa gabanin zaben 2027.

Obi ya kuma gana da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Atiku Abubakar ne ya fara kawo shawarar haɗewar jam’iyyun adawa yayin da yake karɓar baƙuncin Kwamitin Shawara Kan Jam’iyyun Siyasa, IPAC, a watan Nuwamba na shekarar da ta gabata.

Ya bayyana cewa ƙasarnan tana ƙoƙarin tafiya cikin tsarin jam’iyya ɗaya, kuma ya ƙara da cewa dole ne jam’iyyun adawa su haɗa kai don karɓe mulki daga hannun APC.

Ya shaida wa tawagar IPAC cewa: “Kun zo nan yau don ku ce mu yi haɗin gwiwa don inganta dimokuraɗiyya. Amma, gaskiyar magana ita ce dimokuraɗiyyarmu tana tafiya ne zuwa tsarin jam’iyya ɗaya, kuma tabbas kun san cewa idan muka samu tsarin jam’iyya ɗaya, to mu dai kawai mu manta da dimokuraɗiyya.

“Mun ga yanda APC ke ƙara mayar da Najeriya ƙarƙashin mulkin kama-karya na jam’iyya ɗaya. Idan ba mu haɗa kai ba don kalubalantar abin da jam’iyyar mai mulki ke kokarin ginawa, dimokuradiyyarmu za ta sha wahala, kuma sakamakon hakan zai shafi al’ummominmu da ba su zo duniya ba.”

Haka kuma, kwanan nan ne, shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Chief Ralph Okey Nwosu, ya ce shugabannin jam’iyyun adawa suna tattaunawa don gina jam’iyya mai ƙarfi da za ta iya kayar da APC mai mulki a shekarar 2027.

Tarihin haɗin kan jam’iyyu a Najeriya yana cike da rashin nasara, sai dai yanzu, duk da cewa sauran watanni 30 suka rage kafin zaben shugaban ƙasa na ranar 20 ga Fabrairun 2027, idan har jam’iyyun adawa suka warware matsalolinsu suka haɗa kai, za su iya yin nasara kan APC a zaɓen.

Comments
Loading...