For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ziyarar Kwamatin Takarar Shugaban Kasar Atiku Jihar Jigawa, Ta Banbance Tsakanin Tsaki Da Tsakuwa

A Ranar Juma’a 07/01/2022 wani Babban Kwamatin Tsare-Tsare a kan takarar Shugaban Kasa da Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Alh. Atiku Abubakar GCON ya ziyarci jihar Jigawa, musamman domin yada munafar Alh. Atiku Abubakar din dangane da Babban Zaben 2023 dake tafe.

A wannan rana kwamatin ya tsara ne zai ziyarci jihar Jigawa da Yobe da kuma jihar Kano. A jadawalin wannan kwamatin akwai ziyarar bangarori biyu na jamiyyar PDP Reshen jihar Jigawa wato bangaren Tsohon Gwamnan jihar Sule Lamido da kuma bangaren Siyasa da Kulawa na Mallam Aminu Ibrahim Ringim.

Kwamatin ya fara da jihar Yobe inda daga bisani kuma ya shigo jihar Jigawa bisa son ya kammala da jihar Jigawa, kuma ya shiga jihar Kano.

Sai dai kuma kash, bayan kwamatin ya je gidan  Sule Lamido Sule Lamido, ya rike kwamatin tun wajan karfe 2 na rana har zuwa sallar Isha’i wanda kowa ya san hakan ya sabawa hankali da tunanin duk wani mai tunani.

Ko ba a fada ba, an san dalilin yin hakan bai wuce cewa ana son a hana wannan kwamatin zuwa gidan Mallam Aminu Ibrahim Ringim ba. Koda yake koda babu wannan matsalar na tabbatar Sule Lamido bazai taba barin wani abu da zai ciyar da Atiku Gaba yayi Nasara ba.

Koda yake wasu suna ganin kwamatin ya wulakanta mu, amma batun gaskiya kwamatin bai wulakanta ba, face dai ya zo jihar Jigawa ya fita kamar bai shigo ba.

Bisa Al’ada

Bisa al’ada duk inda wannan kwamatin ya je, jagoran wannan tafiyar ya kan fito ya nuna goyon bayansa ga takarar Shugaban Kasa ta Alh. Atiku Abubakar da kuma jamiyyar PDP.

Amma bayan kwamatin ya gama wannan ziyarar, bayanai sun tabbatar mana cewa, an tsoratar da membobin kwamatin cewa, lalle ya kamata su guji tsayawa a ko’ina a hanya wai saboda Arewa ana satar mutane da wannan aka fake aka hana su zuwa gidan Mallam Aminu Ibrahim Ringim da kuma jihar Kano a wannan ranar.

Abin Tambaya

Shin me yasa har yanzu mutanan Sule Lamido basu fito suka sanya wadannan hotunan da aka dauka da ‘yan kwamatin ba, ballantana su nuna sunyi farinciki ko kuma suna goyon bayan kwamatin ba?

Shin yaushe ne mutanen Sule Lamido suka fara goyon bayan Atiku Abubakar bayan kowa yana ganin yadda suka ringa cin mutuncin sa a kwanakin baya bisa zargin cewa shine yake rike da tafiyar mu?

Shin ina maganar da suke cewa Atiku Abubakar ne gatan mu, mu kuma muna fada musu cewa karya ne, Allah ne gatanmu?

Shin ina makomar Tambuwal da aka jima ana masa romon baka ana karbar kudinsa da nufin cewa shine dan takarar Shugaban Kasa da Sule Lamido da mutanensa za su bi?

Shin mutane wace fassara za su yiwa Sule Lamido da magoya bayansa a kan yin shiru kan wannan ziyarar?

Tunani Na

Nidai a tunani na dole ce ta sanya Sule Lamido da magoya bayansa tarbar kwamatin Atiku Abubakar domin sun tabbatar yanzu jamiyyar PDP a jihar Jigawa ba mallakin mutum daya ba ce, don haka idan sun wulakantasu ma akwai inda za su je wanda ma ya fi nasu wajen mutane.

Shawara

Ina bawa kwamatin Atiku da shi Atiku Abubakar shawara a kan su tsaya su bawa kansu amsoshin tambayoyi a kan zuwansu jihar Jigawa riba suka ci ko faduwa? Tunda an ce har kudi suka bada amma basu samu darajar da za’a ko dora hotonsu a Facebook ba, ballantana jaridu duk da cewa lokacin da suka kai ziyarar akwai gidan TV na Channels da NTA da jaridu irin su The Sun da The Nation, amma babu wanda ya ba da labarin ko da a kanun labarai.

Sannan ina bawa Sule Lamido shawara a kan ya gane cewa, yanzu shekarunsa sun wuce ya yi abin da bashi da niyya ko kuma ya yi abin da ba ya so don batawa wani rai.

Karshe

Wannan abu a ganinmu mu nasara ce domin mun sanya mutanen da suke ganin ba mu isa ba sun bawa makiyansu masauki.

Sannan yanzu duniya dole zata yadda cewa, da kafarmu muke zaune a jamiyyar PDP ba Atiku Abubakar ne yake rike da mu ba.

Sannan ko yanzu alamu sun nuna cewa lalle ana tsoronmu domin an san inda ace an bari an zo inda muke da an gane cewa Sule Lamido kwamfalala ne a siyasance a yau.

Daga: Haruna Shu’aibu Danzomo

Comments
Loading...