For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zulum Ya Bada Kyautar Naira Miliyan 20 Ga Iyalan Sojan Da Aka Kashe A Jihar Borno

Daga: Labari Daga Bauchi

A kokarinsa na nuna jimami da karfafa gwiwa ga sojoji da suke yaki domin kawo karshen yakin Boko Haram a jihar Borno. Gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, ya debi tawaga ta musamman zuwa jihar Kaduna domin ziyartar gidan Marigayi Janaral Dzarma Zirkushu.

Tawagar gwamnan ta kunshi sanatoci uku na jihar Borno, Kashim Shettima, Mohammed Ali Ndume da Abubakar Kyari; ta isa rukunin gidajen soji na Ribadu dake jihar Kaduna domin yin ta’aziyya.

Yayin ziyarar ta’aziyyar Gwamna Babagana Zulum, ya baiwa iyalan Janaral Zirkushu  tallafin kuɗi kimanin Naira Miliyan 20, yayin da kuma ya jajantawa mata da ‘ya’yan marigayin, inda ya ce mutanen jihar Borno ba zasu taba mancewa da sadaukarwar gwarazon sojojin ba domin ya mika rayuwarsa ne kan kokarin kare al’umman jihar.

“Hakan ne ya sa muka zo domin mu baku hakuri mu kuma jinjina ma irin namijin kokarin da yayi domin yakar Boko Haram da ISWAP yanda ya jagoran ci rundunar soji mai matukar  muhimmanci sukai ta gwabza yaki har zuwa lokacin da aka cimmasa.”

Gwamnan ya ce, gwamnatin jihar Borno za ta kuma tallafawa sauran iyalan sojojin da aka kashe tare da marigayi janar Dzarma Zirkushu.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, da kwamandan rundunar soji ta Division One, Birgediya Janar T. Opuene, sune suka tarbi Zulum, yayin da ya isa jihar Kaduna.

Suma a nasu bangaren iyalan marigayin da suka hada da matarsa,  Blessing Zirkushu, da kuma ƴaƴanta guda 5, da mahaifiyarsa, Gurdebil Zirkushu, sun tarbi gwamnan cikin girmamawa da nuna jin dadi.

Sun bayyana cewa gwamnan ya mutunta su kuma ya nuna cewa dan’uwan nasu yayi hali mai kyau na sadaukar wa wanda ya cancanci a yaba masa.

Irin wannan ziyarar da ba kasafai ake kaiwa ga iyalan gwarazan sojojin ba wani al’amari ne mai girma da zai karfafa gwiwar sojoji wajen aiki tukuru ga kasarsu, domin hakan zai nuna cewa za a iya tallafawa iyalansu ko da sun rasa tasu rayuwar wajen kare kasar su.

Comments
Loading...