For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Zulum Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2022 Mai Yawan Naira Biliyan 267

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2022 ga majalissar dokokin jihar jiya Talata mai yawan kudi Naira Biliyan 267.

Da ya ke gabatar da daftarin kudirin kasafin kudin, Babagana ya ce an yiwa kasafin take da ‘Kasafin Fatan Alkhairi Domin Daidaituwa Bayan Rikici”.

Gwamnan ya bayyana cewa za a kashe Naira Biliyan 172 a bangaren manyan aiyuka, yayin da za kashe Naira Biliyan 95 a bangaren kananan aiyuka.

Zulum ya bayyana cewa, za ai anfani da kasafin wajen gaggauta kammala gina garuruwan da suka rushe domin samun damar mayar da ‘yan gudun hijira matsugunnansu na asali tare da samar musu ingantacciyar rayuwa.

Comments
Loading...