Daga: DailyTrust
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya yi baddabami, ya kai ziyara wasu cibiyoyin samar da lafiya a ranar Alhamis din nan, inda ya kama wasu ma’aikata na karba tsakanin Naira 8,000 da Naira 10,000 daga marassa lafiya a abubuwan da ake yi kyauta.
Zulum ya kira Kwamishiniyar Lafiya ta jihar, Mrs. Juliana Bitrus, inda ya umarce ta da ta same shi cikin wata motar kai mutane filin jirgi.
Gwamnan ya bar gidan gwamnati da misalin karfe 1:30 na rana ba tare da jerin gwanon motoci ba kuma ba tare da jiniya ba, abin da ya baiwa kowa mamaki.
Yana fita ya nufi sabuwar cibiyar lafiya wadda ya gina ya kuma saka kayan aiki a ciki da ke mazabar Gwange ll a Maiduguri ya kuma samu wasu ma’aikata na karbar kudi kafin su duba marassa lafiya da ba su magani a kan kananan cutuka kamar maleriya.
Zulum ya ce, “ma’aikatan da muka samu a nan, (a PHC na Gwange ll) sun tabbatar da cewa suna karbar Naira 8,000 zuwa Naira 10,000 don duba su a kan maleriya. Tabbas sun mayar da wannan cibiyar lafiyar asibiti mai zaman kansa, kuma hakan ne ya sa mutane suka kauracewa asibitin wadanda ba su da kudin da za su iya biya a nan. Ma’aikatan kawai na karbar kudin ne su saka a aljihunsu.”
Gwamnan ya umarci Hukumar Lafiya Matakin Farko ta Jihar Borno da ta yi kwakkwaran bincike kan lamarin, ta gano masu hanu cikin lamarin da kuma yi musu hukuncin da ya dace.
Gwamna Zulum ya kuma nuna bacin ransa ganin yanda ma’aikaci daya ne ke aiki a cibiyar domin duba marassa lafiya, duk da yawan ma’aikatan ya kai 29 wadanda ke aiki a cibiyar kuma suke karbar albashi.
“Ka taba tunanin da misalin karfe 2:30 na rana, wannan cibiya da muka gina muka sanyawa kayan aiki yanda ya kamata a ce babu kowa. Wannan rashin kyautatawa ba za ta karbu ba. Idan mukai saurin magance ta, zai fi dacewa a wajenmu.” In ji Zulum.
Gwamnan ya kuma zarce zuwa wata cibiyar irin wannan da ke Gwange l, inda ya samu ma’aikata na kan aiki kuma ba sa karbar kudin marassa lafiya.
Gwamnan ya ji dadin hakan, inda ya yabawa ma’aikatan saboda kasancewarsu na gari.
Da ma can yana da al’adar baddabami a lokuta daban-daban har ma tsakar dare domin ganin abin da ke faruwa a asibitoci, da kuma sassafe domin ganin abin da ke faruwa a makarantu don tabbatar da ana aiki yanda ya kamata.
Akwai ma lokutan da Zulum ya ke kai irin wannan ziyara makarantu da ofisoshi da cibiyoyin da ke wajen Maiduguri wadanda sai ya yi tafiyar awanni kafin ya isa.