For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Kwamishinan Hukumar Ƙidaya Ta Ƙasa Tare Da Kame Ƴaƴansa

Ƴan bindiga sun kashe tsohon Kwamishinan Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (National Population Commission, NPC), Mr. Zakari Umaru-Kigbu a Jihar Nasarawa tare da kame ƴaƴansa mata guda biyu.

Wakilin jaridar THE NATION ya gano cewa, lamarin ya faru ne a tsakiyar daren jiya, a gidan Umar-Kigbu da ke Azuba Bashayi ta Ƙaramar Hukumar Lafia a Jihar Nasarawa.

Ƴan bindigar dai sun nemi da a basu kuɗin fansa da ya kai Naira Miliyan 50 kafin su saki waɗanda suka kama.

Wani dangin waɗanda abun ya shafa ya shaidawa jaridar THE NATION cewa, ƴan bindiga ne suka kashe Mr. Umaru-Kigbu a daren da ya gabata, sannan suka yi garkuwa da ƴaƴansa mata guda biyu.

Marigayin mai shekaru 60 a duniya, sojan sama ne mai ritaya.

Kafin kisan da akai masa, yana koyarwa ne a Sashin Koyar da Aikin Jarida na Isa Mustapha Agwai Polytechnic, Lafia (IMAP) kuma tsohon Kwamishinan hukumar NPC ne na ƙasa da ke kula da Jihar Nasarawa.

Wakilin THE NATION ya kuma gano cewar, marigayin ya yi aikin agent wa Labaran Maku a zaɓen fidda gwanin da aka kammala kwanannan na jam’iyyar PDP kafin Labaran Makun ya janye.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun ƴan sanda ASP Ramhan Nansel ya ce, rundunar ƴan sandan sun sami labarin kan faruwar lamarin ne da misalin ƙarfe 12:20 na dare.

Ya ce, ana ci gaba da bincike domin tabbatar da abun da ya faru game da lamarin.

Nansel ya kuma tabbatar da cewa, ƴan bindigar sun kuma yi garkuwa da ƴaƴan marigayi mata guda biyu.

Ya ƙara da cewa, an garzaya da Umaru-Kigbu zuwa Asibitin Ƙwararru na Dalhatu Raf, Lafia domin ceton ransa amma ya cika a can.

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce, rundunar ƴan sandan ba ta da masaniya kan kuɗin fansa na Naira Miliyan 50 da aka ce ƴan bindigar sun nema.

Comments
Loading...