Wasu ƴan bindiga aƙalla goma sun yi garkuwa da wani basaraken gargajiya na Mbutu a Ƙaramar Hukumar Aboh Mbaise ta jihar Imo.
Mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Imo Michael Abattam ya tabbatar wa BBC da faruwar lamarin.
An sace Igwe Damian Nwaigwe a fadarsa da misalin 2:30 na dare.
Waɗandasu da suka shaida lamarin sun bayyana cewa ƴan bindigan sun zo ne cikin motoci inda suka zagaye fadarsa tare da da harbi ba ƙaƙƙautawa har zuwa lokacin da suka sace basaraken.
Rahotanni dai sun ce fadar sarkin ba cikin gari take ba, ta yi nisa da gidajen mutanen ƙauye, wanda hakan ya sa ko da ƴan bindigan suka zo ba su fuskanci wata turjiya ba.