For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴan Bindiga Sun Sace Wani Boka A Anambra

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani shahararren boka ɗan asalin Jihar Anambra, mai suna Chinedu Nwangwu a ɗaya daga cikin otel ɗinsa da ke Ƙaramar Hukumar Idemili ta Arewa.

Bokan da aka fi sani da Akwa Okuko Tiwaraki, na nufin ‘ƙwai mai karya ƙwaran manja’ da Hausa, Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kashe mataimakansa guda biyu a lokacin da aka yi garkuwa da shi a daren Lahadi.

Wata majiya ta ce mutumin wanda ake kyautata zaton yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya ƙarfi a jihar ta Anambra, an yi garkuwa da shi ne cikin sauƙi a otal ɗinsa mai suna Triple P Hotel, tare da bindige wasu muƙarrabansa guda biyu har lahira.

Ana kuma kallon Akwa Okuko Tiwaraki a matsayin mai maganin gargajiya mafi kuɗi a jihar domin a shekarar 2022 ya gina tare da ƙaddamar da otal guda biyu, waɗanda aka ɗauka a matsayin mafiya girma a Oba.

Majiyoyi, sun ce sace shi ya janyo ce-ce-ku-ce da kuma raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana ɗaya daga cikin bokaye mafiya ƙarfi.

Hukumomin ƴan sanda a jihar sun tabbatar da faruwar lamarin, inda Mai Magana da Yawun Ƴansandan Jihar, DSP Toochukwu Ikenga ya ce, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:30 na dare, sai dai daga bisani an sako bokan da aka sace.

BBC HAUSA

Comments
Loading...