For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴansanda Sun Kama Shahararren Ɓarawon Motoci A Kano

Ƴansanda a Kano, sun kama shahararren ɓarawon motoci mai suna Ibrahim Usman ɗan shekara 34 a duniya.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da hakan a sanarwar da DAILY POST ta samu.

Ya ce, jami’an Operation Puff Adder a zagayen da suka saba, a kan Titin BUK sun kama wani da ake zargi tare da wata farar Toyota Hilux

Ya yi bayanin cewa, a sakamakon gwajin farko da aka gudanar, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na satar wannan farar Hilux ɗin a kan Titin Madobi da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano.

SP Abdullahi ya kuma ce, wanda ake zargin yana cikin gungun wasu ɓarayin motoci ne waɗanda suka ƙware a satar motocin mutane a faɗin jihar.

“An samu mukullai 29 a tare da shi da lambobin mota guda 9,” in ji SP Abdullahi.

Ya ƙara da cewa, duk wanda ya san an sace masa mota, to ya sanar a Sashin Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansanda ta Bompai da ke Kano ko kuma ya kira wannan lambar 08105359575.

A nasa ɓangaren, Kwamishinan Ƴansanda na Jihar Kano, ta bakin SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi kira ga al’umma a jihar da suna kulawa da dukiyoyinsu, sannan ya ce, ana ci gaba da bincike domin a kamo abokan aikin wanda ake zargin.

Comments
Loading...