For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴansanda Sun Kama Ƙasurgumin Mai Garkuwa Da Mutane Da Wata Ƴar Leƙen Asirinsu A Zamfara

Rundunar ƴansandan Jihar Zamfara sun kama wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane mai suna Lawali Danhajiya, wanda ya ƙware a yin garkuwa da mutane a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Haka kuma ƴansandan sun samu nasarar kama wata ƴar leƙen asirin babban ɗan bindigar nan da aka fi sani da Dankarami.

Da yake yi wa ƴanjarida jawabi a ranar Juma’a a shalkwatar ƴansanda a Gusau, Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴansandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya ce, ɗan garkuwa da mutanen, Danhajiya ya daɗe yana addabar yankin Saminaka na garin Gusau.

Ya ƙara da cewa, jami’an ƴansandan da ke Yankin Gusau sun yi amfani da bayanan sirrin da suka samu wajen kai wa ga kama babban mai garkuwa da mutanen.

A lokacin da za ai kamun, an samu wani mai suna Mika’ilu Ibrahim ɗan Saminaka da ya gane wanda ake zargin, saboda a lokacin baya a watan Maris na 2023, Danhajiya ya taɓa yin garkuwa da shi a gidansa da ke Saminaka.

Wata mata ma mai suna Aina’u Aliyu ƴar Saminaka ta tabbatar da gane ɗan garkuwa da mutanen saboda ita ma ya yi garkuwa da ita a ranar 22 ga Yunin 2023.

ASP Yazid ya kuma tabbatar da cewar ƴar leƙen asirin da aka kama, Umma Zubairu ƴar shekara 35, ƴansandan sun kamata ne lokacin da ƴanbindigar ke ƙoƙarin kai hari kan ƴansanda a jihar.

Ya ƙara da cewa, za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.

Comments
Loading...