For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ƴansanda Sun Kama Ɓarayin Wayar Lantarki, Shanu, Awaki Da Ƴan-Fashi A Jigawa

Jami’an ƴansanda na Rundunar Ƴansanda ta Jihar Jigawa sun kama wasu da ake zargin ƙwararrun ɓarayin shanu da awaki ne a garin Maigatari.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Shiisu Adam ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi ga manema labarai jiya Talata a Dutse, babban birnin jihar.

DSP Shiisu ya ce, yayin da aka kama waɗanda ake zargi su biyu da shanun da suka sata, an kuma kama wasu su biyu da awakin da su ma suka sata.

Ya ce an yi kamun ne a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta da safe bayan an samu bayanan sirri inda aka kama wani da ake kira Abdullahi Ya’u wanda aka fi sani da Mado ɗan shekara 20, ɗan unguwar Bakin-Kara da kuma wani mai suna Nasiru wanda aka fi sani da Danlin mai shekaru 23 a duniya ɗan unguwar Kofar Arewa duk ɗinsu ƴan garin Maigatari.

Ya ƙara da cewar, dukkansu su biyun an kama su ne a wani kango da ke unguwar Abuja bayan sun yanka wani sa da ake zargin satowa suka yi suka yanka.

DSP Shiisu ya kuma ce, a dai wannan ranar da rana wajen ƙarfe 1, jami’an ƴansanda sun samu nasarar kama wani da ake kira da Hamza Hassan ɗan shekara 20 na unguwar Kattakara da kuma wani ɗan shekara 15 mai suna Mudansiru Isah ɗan unguwar Saminaka duk a garin Maigatari.

Ya ce, an kama waɗannan ne a bakin boda ɗauke da akuyar da suka sata wadda mallakin wani da ake kira da Sani Inusa ɗan Rugar Hardo Sale ce a Ƙaramar Hukumar Maigatari.

Ya ƙara da cewar, a lokacin da ake bincikar waɗanda ake zargin, dukkansu sun amsa aikata laifukan.

KARANTA WANNAN: Wasu Da Ake Zargin Makiyaya Ne Sun Kai Hari Wata Makaranta, Sun Kashe Ango Da Amarya

Ƴansandan na Jihar Jigawa sun kuma samu nasarar kama wasu da ake zargi da aikata fashi da suka haɗa da Buba Ahmadu, Adam Ahmadu da Haruna Ahamadu dukkansu ƴan Sabon Garin Walawa Fulani da ke Ƙaramar Hukumar Birniwa.

Haka kuma a ranar Litinin ƴansandan sun samu labarin cewar wasu mutane sun tone wayar lantarkin da ke kai wutar lantarki makarantar Tsangaya School a yankin Ƙaramar Hukumar Buji.

DSP Shiisu ya ce, an kama Nafiu Adamu, Adamu Idris da Kabiru Alasan dukkansu ƴan ƙauyen Ganta da wayoyin da suka tone, inda ya ƙara da cewar, waɗanda ake zargin sun kuma tona asirin abokan harƙallarsu.

Jami’in Hulɗa da Jama’ar ya kuma ce, Kwamishinan Ƴansandan Jihar Jigawa, Effiom Ekot ya umarci dukkan shugabannin ofisoshin ƴansanda na jihar da su ci gaba da bibiyar guraren ɓuyan ɓatagari a yankunansu.

Comments
Loading...