Jami’an Rundunar Ƴansandan Jihar Ebonyi, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, sun mamayi sansanin Eastern Security Network (ESN), wanda yake kasancewa maɓoyar ƴan haramtacciyar ƙungiyar IPOB, inda suka kashe ƴan ƙungiyar mutum 5.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar Ƴansandan, SP Chris Anyanwu ne ya sanar da hakan ga manema labarai a Abakiliki.
Ya kuma ce, an bibiyi ƴan ƙungiyar ne har maɓoyarsu da ke ƙauyen Isu wanda ke ƙaramar hukumar Onicha ta jihar, ta hanyar haɗin gwiwar jami’an tsaro da suka haɗa da ƴansanda, sojoji da kuma jami’an DSS.
Anyanwu ya kuma ce, jami’an da suka kai samamen, sun samu nasarar kwato bindigu da harsasai da dama, da ma sauran abubuwa.
Ya kuma ce, sumamen, ya samo asali ne bayan ƴan ƙungiyar sai kai hari kan motar jami’an tsaro a ranar Litinin, inda wani jami’i ya rasa ransa.
Ya ƙara da cewa, rundunar ta kuma wasu manyan likitocin gargajiya, da suka haɗa da Itumo Edeh Omukwor, mai shekaru 63, da kuma Irem Ogbeji Nwaduma, mai shekaru 50, daga yankin Okpera Osege na ƙaramar hukumar Ndufu Echara Ikwo da ke jihar.
Mai magana da yawun ƴansandan, ya buƙaci al’umma da su temakawa ƴansandan da bayanan da suka da ce waɗanda suka shafi ɓatagari.