Jami’an ƴansanda a Jihar Kano, a yau Talata, sun tarwatsa masu zanga-zangar nuna ƙin jinin janye tallafin man fetur da Gwamnatin Tarayya ta yi.
Wani da ya shaidawa idanunsa abun da ya faru, ya shaidawa jaridar DAILY TRUST cewa masu zanga-zangar sun fara zanga-zangar kafin zuwan jami’an ƴansanda wajen.

Ya ce, masu zanga-zangar sun taru ne a Gidan Murtala kusa da titin Kofar Nassarawa kwatankwacin kilomita biyu zuwa ofishin Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, KMC da misalin ƙarfe 7 na safiyar yau.
To sai dai amma, lokacin da ƴanjaridu suka isa wajen domin ganewa idanunsu abun da ke faruwa, sun iske jami’an ƴansanda sun mamaye gurin da aka gudanar da zanga-zangar.