For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ɗalibai Da Fusatattun Matasa Na Shirin Yin Zanga-Zangar Tarzoma Kan Matsatsin Da Ake Ciki A Najeriya, In Ji DSS

Sashin Tsaro na Farin Kaya, DSS, a yau Litinin ya bayyana cewar ya gano shirin da wasu suke yi a sassan ƙasar nan da gudanar da zanga-zanga mai ɗauke da tarzoma.

A sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na DSS, Peter Afunanya ya fitar, ya ce, an shirya tayar da tarzomar ne domin a ɓata sunan Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro kan abubuwan da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki.

Bayanan asirin da DSS ta samu sun nuna cewar, masu shirya tayar da tarzomar sun haɗa da wasu ƴansiyasa waɗanda suke ruɗar wasu shugabannin ɗalibai, ƙungiyoyin yankuna, matasa da kuma gungun fusatattun mutane domin su yi aikin.

KARANTA WANNAN: DA ƊUMI-ƊUMI: NLC Za Ta Yi Yajin Aikin Gargaɗi Na Kwana Biyu A Farkon Mako Mai Zuwa

Afunanya ya ce, DSS ta gano waɗanda suke jagorantar shirya tarzomar kuma tana bibiyar lamuransu tare da ƙoƙarin kare su daga jefa ƙasa cikin tashin hankali.

Ya ƙara da cewar, a dalilin hakan, suna bayar da shawara ga shugabannin jami’o’i da sauran manyan makarantu da su hana ɗalibansu shiga cikin abin da zai kawo tsaiko ga zaman lafiyar ƙasa.

Haka kuma su ma iyaye an yi kira gare su da su wa’azantar da ƴaƴansu da sauran waɗanda suke ƙarƙashinsu kan su guji shiga cikin aiyukan da suka saɓa doka.

Comments
Loading...