Ɗan Majalissar Wakilai mai wakiltar Darazo da Ganjuwa daga Jihar Bauchi, Mansur Manu Soro ya ce, zai samar da kayan abinci kyauta ga zawara 2,000 a mazaɓarsa.
Ɗan majalissar ya bayyana hakan ne ga jaridar DAILY TRUST a jiya Laraba, a wata tattaunawa da suka yi.

Ya ce, “Bayan cire tallafin man fetur, ƴan Najeriya sun tsinci kansu cikin mawuyacin hali da ke ƙara tsanani ga matsalolin rayuwarsu.
“Saboda haka, a kan wannan yanayi ne na yanke shawarar samar da tallafin abinci ga mata 2,000 musamman ma zawarawa.