For real, reliable, and timely news updates on national and global events.

Ɗiban Malaman Sa Kai Na J-Teach Ba Mafita Ba Ce Ga Matsalar Ƙarancin Malamai A Jigawa

Daga: Kabiru Zubairu Birnin Kudu

Na daɗe da ƙalubalantar yunƙurin gwamnatin Jihar Jigawa na magance gagarumar matsalar ƙarancin malaman makaranta da tai wa harkar ci gaban ilimin jihar dabaibayi tsawon shekaru na amfani da malaman sa kai (volunteers) a shirin J-Teach. Tun gwamnatin baya ta Badaru Abubakar da ta fara shirin, na gano cewar gwamnati ba ta shirya magance matsalar ƙarancin malaman makaranta a Jigawa ba. Na sani babu wani mai kishin ci gaban harkar ilimi da ci gaban al’ummar Jigawa da zai bai wa gwamnati shawarar yin wannan aika-aikar ga ɓangaren ilimi. Tabbas akwai matuƙar buƙatar gwamnati ta gyara wannan ƙaton kuskuren nan take, sannan ƴan jihar su nuna rashin goyon bayansu ga wannan shirin.

Abun da ya bayyana na dalilin gwamnatin Jigawa na yin shirin J-Teach shine tsoron kashe wa sabbin malaman da za a ɗauka na dindindin kuɗaɗen albashi. Gwamnati ba ta son yin amfani da kuɗaɗen da ake turowa ƴan Jigawa wajen bunƙasa harkokin iliminsu wanda shine mafi muhimmanci a kan zaɓin san ran da gwamnati ke yi na yin wasu aiyuka da suka shafi ci gaban aljihun muƙarrabanta. A bayyane yake cewar, fifiko da ɗinbin kuɗaɗen da aka ware wa harkar ilimin a kasafin kuɗin bana ba a ware don bunƙasa harkar samun ingantaccen ilimi ba, sai dai don harkar yin kwangilolin gine-ginen da zasu samarwa muƙarraban gwamnati kuɗaɗe.

Ko a yanayi na kwafowar da Jigawa tai wa shirin N-Power na Gwamnatin Tarayya wajen yin J-Teach ba ta kwafo daidai ba. Ita Gwamnatin Tarayya a bayyane yake cewar ta samar da shirin N-Power ne domin samarwa matasa mafaka kafin su samu aikin yi ba wai don gwamnati ta samu ma’aikatan da ba ta da su ba. A Jigawa ne gwamnati ta mayar da shi wata hanya ta danniya da hana matasa damar yin aikin gwamnati na haƙiƙa kamar yanda sauran jihohi suke yi ta ƙirƙiro hanyar ƙara ɓatawa matasa lokaci a yunƙurinsu na samu da kuma samarwa al’umma ingantacciyar rayuwa.

KARANTA WANNAN: JERIN SUNAYE: Masu Degree Da Suka Samu Aikin Sa Kai Na J-Teach A Jigawa

Ƴan J-Teach ba ma’aikata ba ne, amma kuma za a ba su aiki kamar sauran ma’aikata wai da nufin gwada ƙwarewarsu, ko a ina aka taɓa yin hakan? Duk shekarun da masu degree su ka ɗebe suna karatu a fannin da su ka karanta, duk gwajin koyarwar da su kai lokacin da suke karatu, duk koyarwar da su kai ta kimanin shekara ɗaya a matsayin NYSC, duk sauran gwagwarmayar rayuwar da su kai – a yau gwamnatin Jigawa ta zo ta ce basu iya komai ba, ba zasu iya koyarwa a makarantun sikandiren jihar ba har sai an gwada su na tsawon lokacin da ba a da tabbacinsa. Wannan a gaskiya rashin adalci ne da rashin mutumta matasa masu ilimi da kuma rashin martaba harkar ilimin al’ummarmu.

Maimakon gwamnatin da al’umma suka zaɓa ta kula da kyakkyawar goben matasansu da ƙananansu, gwamnatin Jihar Jigawa ta Badaru Abubakar da ta Malam Umar Namadi sun taƙarƙare wajen ganin sun durƙusar da ci gaban gatan goben jiharmu. A yanayin da aka ɗauka a jiharmu, matasanmu ya zasu na kai wa shekarun ritayarsu ta aiki ta shekarun rayuwa ba daɗewar aiki ba – kuma su masu jan ragamar gwamnatin sun san illar hakan ga ci gaban ɗan’adam a kan kansa da kuma a al’umma baki ɗaya.

Har yanzu ba a makara ba, gwamnati zata iya gyara wannan kuskure, a yau Gwamna Namadi zai iya sanar da canja tsarin, ya mayar da dukkan ƴan J-Teach cikakkun malaman makaranta, waɗanda zasu hau kan tsarin ƙa’idojin cikakken aiki. Muna fatan hakan daga gare shi, domin kuwa wannan ne kaɗai abun da zai tabbatar da daranjantawar da yake iƙirarin yana yi wa ɓangaren ilimi da sauran ɓangarorin ci gaban al’ummarmu. Mu ma ƴan jihar, ya kamata mu dage da kira, nusarwa da kuma tunatar da gwamnati kan abubuwan da suka dace da ci gabanmu ba kawai mu koma gefe muna gunaguni ko jiran lokacin sabon zaɓe ba. Idan ta kama ma, mu nunawa gwamnati rashin amincewarmu ta hanyar zanga-zangar lumana don Hausawa na cewa, makaho bai san ana ganinsa ba har sai an zungure shi.

Kabiru Zubairu Birnin Kudu

Comments
Loading...